Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar

Wasannin Duniya Ba Fira ministan kasar ta Spain ya bayyana hakan ne dai a yayin da yake nuna jin dadinsa danagen da gagarumar Muzaharar da

Wasannin Duniya Ba

Fira ministan kasar ta Spain ya bayyana hakan ne dai a yayin da yake nuna jin dadinsa danagen da gagarumar Muzaharar da mutanen kasar su ka yi ta nuna kin amincewarsu da shigar kasar ta Yahudawa cikin tseren kekune.

Fira ministan kasar ta Spain Pedro Sánchez Pérez ya ce: ” Har zuwa lokacin da za a kawo karshen kisan kiyashi a Gaza, bai kamata a kyale Isra’ila ta rika shiga cikin gasar wasannin kasa da kasa ba.

A yau litinin ne dai Fira ministan kasar ta Spain ya gabatar da jawabi gabanin taron ‘yan majalisa masu wakiltar jam’iyyun gurguzu, ya yi ishara da taho mu gamar da aka yi a tsakanin masu kin jinin kisan kiyashin da HKI take yi wa Falasdinawa da masu goyon bayanta, sannan ya kara da cewa; a kodayaushe ba mu aminta da tashin hankali ba.

Mutane 20 ne dai su ka jikkata a yayin wannan taho mu gama din a babban birnin kasar ta Spain,Madrid.

Fira ministan Pedro Sánchez Pérez   ya kuma yi wa hukumomin wasanni na duniya tamabya da cewa; Me ya sa aka haramtawa Rasha shiga cikin wasannin kasa da kasa saboda yakin Ukiraniya,amma ba a kori Isra’ila ba?.

Al’ummar kasar Spain da mahukuntanta suna cikin na gaba-gaba a cikin nahiyar turai wajen nuna kin amincewa da yi wa mutanen Gaza kisan kiyashi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted