Search
Close this search box.

Duniyarmu A Yau: Farmakin Sojojin HKI A Yankin Yamma Da Kogin Jodan, Tare Da Kiran MDD Na Ta Dakatar Da Shi

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu sauraro za su kasance tare da mu.

///… Madallah, masu sauraro shirimmu na yau zai yi Magana ne dangane da ‘ayyukan soje mai tsanani wanda gwamnatin haramtacciyar kasar Isar’ila (HKI) ta fara a yankin yamma da kogin Jordan da kuma kiran da majalisar dinkin duniya (MDD) ta yi na ta dakatar da kissan kiyashin da ta ke yi a can.

Kamfanin dillancin labaran Sahab na hukumar gidajen radiyo da talabijin ta kasar Iran ya nakalto babban sakataren MDD Antonio Guterres ya na kira ga gwamnatin HKI ta kawo karshen aikin soje masu tsanani da ta fara a yankin yamma da kogin Jordan na kasar Falasdinu da aka mamaye.

Estefan Dujoric, kakakin babban sakataren MDD a cikin wani bayanin da ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana mutukar kaduwarsa da abinda yake faruwa a yankin yamma da kogin Jordan. Babban sakataren ya yi allawadai da asarar rayuka, musamman na yara kanana wadanda sojojin HKI suka haddasa mutuwarsu a hare haren da suka kai kan wasu garuruwa a yankin.

Guterres ya bukaci HKI ta yi aiki da dokokin kasa da kasa wadanda suka hada da kare hakkin bil’adama, da kuma ta tabbatar da cewa ta kiyaye rayukan fararen hula da kuma amince su a duk hare haren da sojojin ta suke kaiwa kan falasdinawa a yankin.

Babbann sakataren ya bukaci sojojin HKI su yi amfani da karfi ne kawai don kare kansu, kada su kashe duk wanda suka hadu da shi daga cikin falasdinawa a faramakin da suke kaiwa kansu a yankin yamma da kogin Jordan.

A safiyar ranar Laraba ce dai sojojin HKI suka fara aikin soje mai tsanani a arewacin yankin yamma da kogin Jordan na kasar Falasdinu da suka mamaye.

A halin yanzu dai sojojin yanhudawan sun fara aikin soje mai tsanani ne a garuruwan Jenin, Nurushams da kuma Al-fari’ah na arewacin yankin yamma da kojin Jordan, kuma ya zuwa yanzun sun kashe falasdini akalla 11, a sansanonin yan gudun hijira na Falasdinawa guda uku, wato Al-fari’ah, Jenin da kuma Nurushams.

Kafafen yada labarai na yahudawan sun bayyana cewa, wannan aikin sojojin da suka fara a yankin yamma da kogin Jordan shi ne mafi girma tun shekaru 22 da suka gabata a wannan yankin.

Sannan jaridar Yadi’ud-Oharnood, ta gwamnatin HKI ta bada labarin cewa, wannan aikin sojen da sojojin yahudawan suka fara a yankin yamma da kogin Jordan zai dauki wasu kwanaki masu yawa tana ci gaba da shi. Banda haka wata tashar radiyo ta Yahudawan ta bayyana cewa aikin sojen da HKI ta fara a yankin yamma da kogin Jordan shi ne mafi girma tun boren intifada na shekara ta 2002.

Tun bayana fara yakin Tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata, sojojin HKI sun kama falasdinawa fiye da 10,000 a yankin yamma da kogin Jordan kadai, sannan a shafinsa na X, ministan harkokin wajen HKI Isra’il Katz ya bukace a kori falasdinawa gaba daya daga yankin yamma da Kogin Jordan.

Wani abin lura a nan shi ne, bayan da sojojin HKI sun kasa cimma manufofinsu a yakin Gaza, kusan watanni 11 da suka gabata, wadanda suka hada da murkushe Hamas, kwace yahudawan da suke tsare a hannun Hamas, da kuma kwace iko da zirin Gaza, a halin yanzun kuma sun fara wani sabon yaki a yankin yamma da Kogin Jordan da sunan murkushe Falasdinawan da take kira ‘yan ta’adda’.

Wasu masana suna ganin manufar aikin sojen da sojojin HKI suka soma a yankin yamma da kogin Jordan, itace korar Falasdinawa daga yankin zuwa cikin kasar Jordan.

Tare da haka zata kwace fileyensu na noma da kuma gidajensu, su bawa yahudawan da suke kawowa daga kasashen waje wadanda zasu maye gurbinsu.

Kungiyoyin Falasdinawa wadanda suke yaki da sojojin HKI a Gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan sun yi All..wadai da sabon aikin sojen da sojojin HKI suka kaddamar a yankin Yamma da Kogin Jordan. Sun kuma kara da cewa, maimakon sojojin yahudawan su fuskanci mayakan wadan nan kungiyoyi masu gwagwarmaya, sai suka koma kan kashe mata da yara a gidajensu, wadanda basa dauke da makami.

Kungiyoyin Hamas da Jihadul Islami sun bayyana cewa, aikin sojen HKI a yankin yamma da Kogin Jordan yana nufin kwace iko da garuruwan da suke gewaye da masallacin Al-aksa ko birnin Kudus, saboda su aikwatar da munanan manufofinsu a masallacin da kuma birnin Kudus.

Gwamnatin kasar Amurka dai, kamar yadda ta saba, a ayyukan sojen da HKI ta fara a yankin yamma da kogin Jordan, ta rufe idanunta kan duk abinda yake faruwa a can, ta fadawa yahudawan su rage yawan kissan Falasdinawa kadai.

An nakalto wani Jami’in fadar ‘white House’ yana cewa, gwamnatin Amurka tana ganin HKI tana da hakkin kare kanta, abinda Amurka take bukata shi ne ta rage yawan kissan fararen hula a bainda take yi a yankin. Wannan ya nuna cewa HKI ta fara wannan farmakin na yankin yamma da kogin Jordan ne tare da amincewar gwamnatin Amurka.

A kasashen Turai kuma, wasu daga cikinsu sun bukaci HKI ta kawo karshen yaki a yankin yamma da Kogin Jordan, daga cikin akwai kasar Beljika da kuma jami’i mai kula da al-amuran harkkin wajen na tarayyar Turai, wato Josept Borrell.

Masana suna ganin, a bisa abinda jami’an gwamnatin HKI suka bayyana ya zuwa yanzu, ana iya cewa manufar gwamnatin HKI a aikin soje na yankin yamma da kogin Jordan ita ce, korar Falasdinwa masu yawa daga yankin, ta yadda adadinsu zai yi kasa sosai, a yankin. Wanda kuma hakan zai bawa sojojin yahudawan iko da yankin da birnin Qudus, sannan sauran falasdinawa a yankin ba za su iya tabuka kome be a yankin.

Don haka idan kasashen duniya musamman kasashen musulmi basu tashi tsaye ba, suka takurawa HKI ba, duniya tana ji tana gani za’a sake korar miliyoyin Falasdinawa daga kasar Falasdinu da aka mamaye.

A bisa dokokin kasa da kasa dai yankin yamma da kogin Jordan na kasar Falasdinu ne, wanda sojojin HKI suka kwace a yakin shekara 1967. Kuma kudurin kwamitin tsaro na MDD mai lamba 242 ya bayyana haka a fili, kan cewa yankin yamma da kogin Jordan daga cikin har gabacin birnin Kudus mallakin Falasdinawa ne. Amma HKI tare da cikekken goyon bayan Amurka da sauran kasashen yamma, ta take dukkan wadannan dokokin kasa da kasa, Tana kokarin kara korar wasu miliyoyin Falasdinawa daga kasarsu.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yai sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu, wassalamu allaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments