Tashin Farashin Mai A Kasuwar Duniya Sakamakon Rikin Gabas Ta Tsakiya

Farashin danyen mai a kasuwar duniya ya tashi sakamakon fargabar barkewar mummunan yaki a yankin Gabas ta Tsakiya. A halin da ake ciki farashin ɗanyen

Farashin danyen mai a kasuwar duniya ya tashi sakamakon fargabar barkewar mummunan yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.

A halin da ake ciki farashin ɗanyen mai nau’in Brent ya ƙaru zuwa Dala 77.

Farashin ɗanyen mai ya tashi ne bayan Shugaba Joe Biden na ƙasar Amurka ya ce suna tattaunawa kan yiwuwar taimaka wa Isra’ila domin kai wa ƙasar Iran hari.

Sakamakon haka ake fargabar ɓarkewar mummunan yaƙi a Gabas ta Tsakiya a sakamakon cacar baka da kuma harin da ƙasar Iran ta kai wa Isra’ila, wadda ita ma take kai hare-hare a zirin Gaza da kuma kan kungiyar Hisbullah a ƙasar Lebanon.

Amma masu hasashe din bayyana cewa farashin zai sauka saboda Amurka banda isasshen mai  sannan Libya ta shawo kan matsalar da ta haka fitar da mai daga ƙasar na tsawon wata guda.

A watan a Dismaba kuma ake sa ran Ƙungiyar kasashe masu arzikin mai, OPEC+, wadd a Saudiyya ke jagoranta kuma za ta ƙara yawan ɗanyen man da take haƙowa.

Iran ta yi wa Isra’ila ruwan makamai masu linzami harin tare da nuna mata yatsa ne bayan Isra’ilar ta kashe Hassan Nasrallah, shugaban Hisbullah ta ƙasar Lebanon da wasu manyan jagororin ƙungiyar wadda Iran ke goyon baya.

Hain da ta bayyana a matsayin ɗaukar fansa kan kashe-kashen da Isra’ila ke wa jagororin ƙungiyoyin gwagwarmayar Larabawa da ke da goyon bayan Iran a Zirin Gaza da Lebanon da Yaman ya haifar da zullumi ga masu zuba jari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments