Faransa Ta Yi Tir Da Zancen Smotrich Na HKI Akan Shimfida Iko A Yammacin Kogin Jordan

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar da bayani da a ciki ta nuna kin amincewarta da furucin da ya fito daga ministan kudi na HKI,

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar da bayani da a ciki ta nuna kin amincewarta da furucin da ya fito daga ministan kudi na HKI, Bezalel Smotrich yana cewa, Isra’ila za ta shimfida ikonta akan yammacin Kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labarun Anadoul ya Ambato ma’aikatar harkokin wajen ta Faransa tana cigaba da cewa; Maganganu irin wadanda Smotrich ya furta suna cin karo dokokin kasa da kasa da kuma kokarin a ake yi na tsagaita wutar yaki a cikin yankin.

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai smotrich ya bayyana cewa, ya bayar da umarni ga bangaren masu kuma da matsugunnai da su fara shirin gina muhimman cibiyoyi a yammacin kogin Jordan.

Ma’aikatar harkokin wajen Faransan ta cigaba da cewa; Kasar tana nan akan bakanta na ganin an kafa kasar Falasdinawa, da hakan yake a matsayin abu mai yiyuwa.

A karkashin dokokin kasa da kasa da kudurorin MDD, yammacin kogin Jordan ne wurin da za a kafawa Falasdinawa kasarsu daura da abinda ake kira “Isra’ila”.

A cikin watan Yuli na wannan shekarar koton duniya ta bayyana cewa, kutsen da Isra’ila take yi a cikin yankunan yammacin kogin Jordan ba ya kan doka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments