Search
Close this search box.

Falasdinu: Dubban Falasdinawa Ne Suka Gidanar Da Sallar Jumma A Masallacin Al-Aksa

Falasdinawa kimani dubu 30 ne suka gudanar da sallar Jumma’a a masallacin Al-aksa a jiya Jumma’a. Kamfanin dillancin labaran ‘Falasdinul Yau’ ya bayya na cewa

Falasdinawa kimani dubu 30 ne suka gudanar da sallar Jumma’a a masallacin Al-aksa a jiya Jumma’a.

Kamfanin dillancin labaran ‘Falasdinul Yau’ ya bayya na cewa falasdinawa kimani dubu 30 ne suka gudanar da sallar jumma’a a masallacin al-akasa a jiya. Wannan duk tare da takaita masu shiga masallacin alaksa da sojojin HKI suka yi.

Labarin ya kara da cewa sojojin HKI sun sanya shingaye da dama a kan hanyoyin shiga masallacin , don hana falasdinawa isa masallacin. Amma duk da haka dubu 30 sun isa masallacin sun kuma gudanar da sallar jumma’a .

Jami’am tsaron hki sun yi kokarin hana falasdinawa isa masallacin al-aska tun da dadewa, amma Falasdinawa daga yankunan daban daban na yankin yamma da kogin Jordan.

Kafin haka dai ministan harkokin tsaron cikin gida na HKI Itaamar Bin Guyir ya bada umurnin a takaita yawan falasdinawa da suke zuwa masallacin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments