Akalla Falasdinawa 20 ne aka kashe tare da raunata wasu da dama a jiya Laraba a wani sabon kisan kiyashi da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a wani gidan cin abinci na kasar Thailand da wata shahararriyar kasuwa a yammacin birnin Gaza. Sannan suka ci gaba da kai wasu hare-haren wuce gona da iri kan yankunan zirin Gaza a rana ta 213 a jere.
Majiyoyi watsa labarai a Gaza sun rawaito cewa: Jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun kai wani hari kai tsaye kan gidan cin abinci na kasar Thailand da wata kasuwa mai farin jini da ke kusa, lamarin da ya yi sanadin shahadan mutane da dama da kuma jikkata wasu na daban yawancinsu fararen hula, a wani mummunan yanayi da ke nuni da yadda sojojin mamayar Isra’ila ke nuna rashin kula da rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Wannan kisan kiyashi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tabarbarewar zubar da jini, inda adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren bama-baman da sojojin mamaya suka kai kan wasu makarantu uku a sansanin ‘yan gudun hijira na Bureij da kuma gabashin birnin Gaza a cikin ‘yan sa’o’in da suka gabata suka kai mutane 49, wadanda akasarinsu yara ne, mata da kuma tsofaffi.