Falasdinawa Sun Bukaci A Hana HKI Halattar Gasannin Olympic Na Paris 2024

Kwamitin gasar Olympic na kasar Falasdinu ya rubuta wasika zuwa ga kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa tare da bukatar a kori HKI daga

Kwamitin gasar Olympic na kasar Falasdinu ya rubuta wasika zuwa ga kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa tare da bukatar a kori HKI daga wasannin Olympic na kasa da kasa wanda za’a gudanar a birnin Paris na kasar Faransa daga ranar 26 ga watannan da muke ciki.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto kwamitin Olympic na Falasdinu na fadar haka a safiyar yau Talata, ya kuma kara da cewa ya bukaci shugaban kwamitin Olympic na kasa da kasa, Tomas Bokh da ya hana tawagar yan wasan HKI halattar gasar Olympic na Paris 2024 saboda kotun kasa da kasa ta CCJ ta yanke hukuncin cewa HKI kasa ce yar mamaye, kuma mamayar da takewa kasar Falasdinu ya haramta.

Labarin ya kara da cewa tun bayan fara yakin tufanul aksa, sojojin yahudawan sun kashe yan wasa daban daban Falasdinawa akalla 400 ya zuwa yanzu. Kuma sun lalata wuraren  wasanni da dama.

A ranar 26 ga watan Yulin da muke ciki ne zuwa 11 ga watan Augusta na wannan shekara  za’a gudanar da wasannin Olympic na wannan shekara ta 2024 a birnin Paris na kasar Faransa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments