Falasdinawa 60 Ne Suka Yi Shahada A Gidajen Kurkukun Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Jaridar Wall Street Journal ta Amurka ta bayyana cewa: Fursunonin Falasdinawa 60 ne suka mutu a wuraren da ake tsare da su a haramtacciyar kasar

Jaridar Wall Street Journal ta Amurka ta bayyana cewa: Fursunonin Falasdinawa 60 ne suka mutu a wuraren da ake tsare da su a haramtacciyar kasar Isra’ila saboda azabtarwa

Jaridar Wall Street Journal ta tabbatar da mutuwar fursunonin Falasdinawa da dama a lokacin da suke tsare a hannun sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila tsakanin ranar 7 ga watan Oktoban bara zuwa ranar 2 ga watan Yulin da ya gabata.

Jaridar ta bayyana cewa: Fursunoni 44 ne suka mutu a wuraren da ake tsare da su a barikokin sojin mamaya, yayin da wasu karin fursunoni 16 suka rasa rayukansu a gidajen yari da ake tsare da su saboda fuskantar dangogin azabtarwa.

Jaridar ta nakalto wata takarda da shugaban hukumar tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila ta (Shin Bet) yayi gargadin cewa: Ka’idojin tsare Falasdinawa a haramtacciyar kasar Isra’ila na iya sabawa yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan azabtarwa.

Rahoton kare hakkin dan Adam ya bayar da rahoton tabarbarewar yanayi a gidajen yarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, musamman a sansanin Sasde Teman, inda aka fuskanci azabtarwa da cin zarafin fursunonin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama daga cikinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments