Falasdinawa 40,000 Sun Yi Sallar Juma’a A Masallacin Kudus Duk Da Killace Shi

Duk da killace Masallacin Al-Aqsa da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi, Falasdinawa 40,000 ne suka gudanar da sallar Juma’a a ciki a yau Dubban

Duk da killace Masallacin Al-Aqsa da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi, Falasdinawa 40,000 ne suka gudanar da sallar Juma’a a ciki a yau

Dubban al’ummar Falasdinu ne suka gudanar da sallar Juma’a a Masallacin Al-Aqsa mai albarka, bisa la’akari da tsauraran matakan da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka dauka na neman hana shiga cikin Masallacin.

Ma’aikatar Kula da Wurare na Musulunci da ke birnin Qudus ta kiyasta cewa: Falasdinawa kimanin dubu 40 ne suka gudanar da sallar Juma’a a cikin Masallacin Al-Aqsa a yau.

Majiyar cikin gida ta watsa rahoton cewa: Da dama daga cikin wadanda aka kora daga masallacin na Al-Aqsa da wadanda aka hana su shiga cikinsa, sun yi sallar Juma’ar ce a kusa da kofar Asbad, duk da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun dauki matakin wuce gona da iri kan wasu da dama daga cikinsu.

Tun bayan fara kai hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Falastinu a Zirin Gaza da gabar yamma da kogin Jordan, ciki har da birnin Qudus a watan Oktoban shekara ta 2023, sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka dauki tsaurara matakan tsaro a kofar shiga Masallacin na Al-Aqsa da kuma hanyoyin shiga tsohon birnin na Qudus, kuma a wasu lokuta ma suna hana Falasdinawa da mazauna yankunan da aka mamaye tun a shekara ta 1948 shiga cikin masallacin don gudanar da ibada.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments