Kamfanin dillancin labarai na Irna ya nakalto cewa iyalan yahudawan da dakarun kungiyar gwagwarmaya suka yi garkuwa da su, sun gudanar da zanga zangar nuna kin jinin gwamnatin Natanyaho kana sun bukaci agaggauta kulla yarjejeniyar musayar fursunoni da kungiyar Hamas .
Daga lokacin da aka kaddamar da harin guguwar Aqsa a raar 7 ga watan Oktoba shekarar da ta gabta zuwa yanzu iyalan wanda aka yi garkuwa da yan uwansu suka dora alhakin duk wani tsaiko da ake samu ga fagen siyasa da na tsaro kan gwamnatin Natanyaho , kuma sun soki yadda kwamandojin soji isra’ila ke tafiyar da yaki a gaza.
Majiyar labaran HKI ta sanar da jikkatar sojojinta guda 11 , a ci gaba dauki ba dadi da suke yi da dakarun sojin kungiyar Hamas, haka zalika sun kara da cewa kimanin sojojin isra’ila guda dubu 3 da 305 ne suka jikkata, halin da dama daga cikinsu ya yi muni sosai,