A Amurka dubban jama’a ne suka shiga zanga zanga gaban fadar White House, domin nuna goyan Falasdinu da kuma kin jinin halayyar mahukuntan kasar da suka ce suna da hannu a kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza.
Masu zanga zangar sun katange fadar shugaban kasar da jan kale, suna masu danganta hakan da jan layin da a kwanakin baya shugaba Biden, ya ce bai zai amince da shi ba idan sojojin Isra’ila suka kai farmaki a Rafah.
Ga masu zanga-zangar, shugabannin Amurka, musamman Joe Biden, suna da hannu a kisan kare dangi da aka fara watanni 8 da suka gabata.
A wani labarinb kuma an yi irin wannan zanga zanga a titunan biraren Paris da Lyon na kasar Faransa.
Isra’ila dai na ci gaba da kai hare-hare Gaza da kuma Rafah, duk da kirare-kirayen da kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa dama kotun duniya ke yi na ta dakatar da hakan.
Wasu alkalumman da Hamas, ta fitar a baya bayan nan sun nuna cewa mutum kimanin 210 ne suka rasa rayukansu sannan wasu sama da 400 suka jikkata sakamakon farmakin da Isra’ila ta kai a yankin sansanin Nousseirat, inda ta kwato wasu ‘yan kasarta daga cikin wadanda ake garkuwa dasu.
Akalla Falasdinawa 36,801 galibi yara da mata ne aka kashe tare da jikkata wasu mutum 83,680 a yakin da Isra’ila ta fara a ranar 7 ga Oktoba, 2023 bayan harin ba-zata da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kai.