Denmark Da Greenland Sun Bukaci Trump Ya Kawo Karshen Maganar Banza Na Kwace Greenland

Firay minitocin kasashen Denmark da Greenland sun bukaci shugaban Amurka Donal Trump ya kawo karshen maganganun banza da yake yi na cewa zai kwace kasar

Firay minitocin kasashen Denmark da Greenland sun bukaci shugaban Amurka Donal Trump ya kawo karshen maganganun banza da yake yi na cewa zai kwace kasar Greendland, inda suke ganin wadannan kalaman basu dace ba kan wata kasa mai zaman kanta a duniya.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban Amurka Donal Trump ya sake nanata bukatar kwace kasar Greenland a wata hirar da yayi da yan jaridu a ranar Lahadi a lokacinda yake cikin jirgin saman shugaban kasa na Airforce One. Inda yake cewa muna bukatar kasar Greendlanda don tsaron kasar Amurka.

Firay ministan kasar Danish ko Denmark Mette Frederiksen ya rubuta a shafinsa na Facebook, kan cewa bai kamata shugaba Trump yayi wannan maganar ba kan kasa wacce take da cikekken yenci, kumabai da hakkin kwatar dukkan kasashen da yakebukata a duniya ba.

Frederiksen ya ce kasar Denmark mamba ne na kungiyar tsaro ta NATO kuma yankin greendland bangare ne na kasar don haka yankin yana da kariya na tsaron kungiyar NATO a matsayin bangare na kasar Denmark.

Ya yi kira ga shugaba Trump ya daina maganganun da yake yi don Greenland aba na sayarwa bane kamar yadda kasashen duniya da dama suke maganar cewa su ban a sayarwa bnane.

Har’ila yau Firai ministan Greend landa Jens-Frederik Nielsen ya maida martanmi da cewa shugaban kasar Amurka da yayi maganar yana bukatar Greendlanda kumayana hadamu da kasar Venezuela ba wai bai dace ba kawai, saidai rashin mutuinta kasarmu ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted