Kungiyar gwagwarmayar Musulunci Hizbullah ta sanar da shahadar daya daga cikin kwamnadojinta Ibrahim Mohammad Qubaisi wanda aka fi sani da ‘Hajji Abu Musa’ daga garin Zebdine da ke kudancin kasar Lebanon.
Ya yi shahada ne a lokacin da jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka kai hari a kudancin birnin Beirut a wannan Talata.
An haife shi a garin Zebdine da ke kudancin Lebanon a shekara ta 1962.
Ya shiga sahun kungiyar Hizbullah tun daga lokacin da aka kafa kungiyar a shekarar 1982.
Ya ci gaba da gudanar da harkokinsa na gwagwarmaya a cikin kungiyar tun daga wancan lokaci har lokacin shahadarsa, kamar yadda kuma ya taka rawar gania ayyuka da dama na kungiyar a tsawon wadannan shekaru, inda ya zama daga cikin manyan kwamandojinta afagen daga.
Shi ne babban kwamandan Rukunin mayaka na rundunar a cikin Hizbullah, wadanda suke gudanar da ayyukan a yankin (arewacin Kogin Litani) tsakanin 2001 zuwa 2018.
Ya taka rawa matuka wajen samar da makamai masu linzami ga kungiyar Hizbullah.