Tare da cewa jam’an tsaron kasar ta Amurka suna kama da kuma amfani da karfi akan daliban jami’oin Amurka, sai dai duk da haka har yanzu suna cigaba da nuna kin amincewarsu da yadda gwamnatin kasarsu take cigaba da marawa HKI baya, a kisan kiyashin da take yi wa Falasdinawa.
Daga cikin jami’oin na Amurka da daliban suke zaman dirshan na nuna goyon Falasdinawa da kawai Columbia, a New york, Harvard, Texas, Brown, Washington DC,Goerge Town, da Jami’ar Carlifonia Ta Kudu. A halin da ake ciki a yanzu harabobin wadannan jamio’in sun zama filin dagar fada a tsakanin dalibai da ‘yan sanda, inda a kowace rana ake kama wasu ko kuma raunana su ta hanyar duk da kulake