Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran (IRGC) sun sami nasarar kakkabo jirgin yaki na Amurka wanda ake sarrafashi daga nesa samfurin MQ-9 karo 54 a dai daimashigar ruwa ta Hurmuz.
Jami’in hulda da jama’a na dakarun masu kula da sararin samaniyar kasar a yankin Hurmuz, ya bada wannan a safiyar yau Talata ya kuma kara da cewa, dakarun nasa sun auna sun kuma kakkabo jirgin ne a lokacinda yake shawagi yake kuma daukan hotuna na leken asiri a mashigar ruwan. Banda haka ya ce sun yi amfani da sabbinin makaman kakkabo jiragen sama na zamani.
Labarin ya kara da cewa jirgin yaki irinsa da dakarun suka kakkabo kimanin wata guda da ya gabata ne a kuma sararin samaniyar lardin na Hurmus, wato MQ-1 mai leken asiri da daukar hotunun leken asiri.