Dakarun IRGC Na Kasar Iran Sun Ce: Ba’a Taba Tsaida Samar Da Makamai Masu Linzami A Kasar Ba Ko Na Rana Guda

Iran ta ci gaba da kera makamai masu linzami a kasar, kuma bata dakatar da hakan ba, ko da na rana guda, inji kakakin rundunar

Iran ta ci gaba da kera makamai masu linzami a kasar, kuma bata dakatar da hakan ba, ko da na rana guda, inji kakakin rundunar IRGC a wani jawabin da yayiwa yan jaridu a atisayen sojojin kasar da ke gudana a halin yanzu a tsakiyar kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Burgediya Janar Ali Mohammad Naeini, kakakin rundunar ta IRGC yana fadar haka a jiya litinin a harssa da kafafaen yada labarai. Ya kuma kara da cewa, manufar atisayen na yanzu itace gwada karfin sojojin kasar, na yaki saboda barazanan da kasar take fuskanta ta bangarori da dama, wadanda suka hada da yan ta’adda, HKI da kawayenta da sauransu.

Ya kara da cewa wannan itisayen,! Ya fi kama da yaki da gaske, kuma suna fatan wannan atisaiyen zai yi tasiri a zukatan makiya sosai.

Janar Ali Mohammad Naeini, ya ce atisayen wanda aka sanyawa suna ‘Annabi mai girma'(s),  yana kamar mayar da martani ne ga HKI, saboda hare-haren da ta kaiwa Iran a ranar 26 ga watan Octoban shekarar da ta gabata.

Da kuma nuna mata cewa sojojin kasar Iran sun fi karfinta.

Naeini ya kammala da cewa  nan da yan kwanaki ko kuma makonni HKI za ta gamu da wasu karin makamai masu linzami daga JMI, kari kan wadanda take fama da su daga kasar Yemen a halin yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments