Dakarun na kungiyar ta Hizbullah sun fitar da bayanin na farko bayan tsagaita wutar yaki, wanda kuma shi ne karo na 4,638 tun fara yaki daga shekarar da ta gabata, wanda ya kunshi yadda yakin ya riga gudana.
Bayanin ya ce; Dakarun gwagwarmayar msulunci sun amsa kiran babban magatakarda, kuma shahidinta mafi girman matsayi sayyid Hassan Nasrallah, rahamar Allah a gare shi, da kuma wanda yake rike da tuta bayansa Sheikh Na’im Kassim, Allah ya kare shi, ta aiwatar da hare-hare domin kare al’ummar Falasdinu masu tsayin daka, da gwgawarmayarsu mai jarunta, haka nan kuma domin kare Lebanon.
Bayanin ya ce;tun daga farmakin guguwar Aksa, a ranar 8-10-2023,gwagwarmayar musulunci ta kai hare-hare fiye da 4,637 ( wadand aka sanar da su) a cikin kwanaki 414, da hakan yake nufin bisa kirdado a kowace rana an kai hari sau 11.
Daga cikin wadannan hare-haren da akwai 1,666 da aka kai wa-abokan gaba,- tun daga fara kawo wa Lebanon hari gadan-gadan da kuma fara farmakin “Ma’abotan karfi” da ya fara daga ranar 17-09-2024. Hakan yana nufin cewa bisa kirdado a kowace rana ana kai wa –abokan gaba hare-hare har sau 23.
Bugu da kari wuraren da aka kai wa hare-haren sun kunshi barikokin soja, sansanoni da birane. Hare-haren sun kunshi yankunan da suke kan iyaka da Falasdinu har zuwa gaba da Tel Aviv. Haka nan kuma fuskantar ‘yan mamaya a cikin kasar Lebanon.
Asarar da aka yi wa ‘yan mamaya daga ranar da su ka fara kutse cikin Lebanon ta kunshi kashe sojoji 130, da jikkata wasu 1,250. Tarwatsa tankokin Mirkava 59, da motocin buldoza na soja 11. Sai motocin Hummer 11, sai motoci masu silke biyu da motar jigilar 1.
Bugu da kari ‘yan gwgawarmayar sun harbo jirage marasa matuki samfurin “Hermes 450” guda 6, sai kuma wasu jiragen marasa matuki samfurin “Hermes 900 guda 2 da wani jirgin na leken asiri samfurin Quadcopter guda 1.
Wani abin yin ishara da shi anan shi ne cewa wannan asarar ba ta hada asarorin da aka yi wa abokan gaba a cikin barikoki da kuma sansanoninsu na soja ba, ko kuma a cikin matsugunin ‘yan share wuri zauna.