Dakarun Kungiyoyin gwagwarmayar al’ummar Iraki sun ce sun kai wasu sabbin hare-hare na ramuwar gayya kan wuraren da Isra’ila ta mamaye a cikin yankunan Falastinawa.
Kungiyar masu fafutukar yaki da ta’addanci ta kasar Iraki ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
Kungiyar ta ce ta yi amfani da jirage marasa matuka wajen kai hari kan wani muhimmin wuri da Isra’ila ta mamaye a gabar tekun Dead Sea.
Kungiyar ta ce hare-haren na mayar da martani ne ga kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa fararen hula a Gaza da suka hada da mata da yara da kuma tsofaffi.
Kungiyar ta Iraki ta sha alwashin ci gaba da kai hare-hare na ramuwar gayya a kan wuraren da Isra’ila ke ci gaba da mamayewa na Falastinawa da kuam sansanonin da suka kafa a cikin wadannan wurare.
Har ila yau, kungiyar ta kai hari kan sansanonin sojojin Amurka a Iraki da makwabciyarta Syria a matsayin ramuwar gayya ga goyon bayan da Washington ke ba wa Isra’ila kisan kare dangi a Gaza.