Dakaru Masu Gwagwarmaya A Gaza Sun Ci Gaba Da Fafatawa Da Sojojin HKI A Rana Ta 252 Da Fara Yakin Tufanul Aksa

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto yan rahotanninta daga Gaza suna cewa a ranar ta 252 da fara yakin Tufanul Aksa,  dakarun

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto yan rahotanninta daga Gaza suna cewa a ranar ta 252 da fara yakin Tufanul Aksa,  dakarun Saraya Kudus na kungiyar Jihadul Islami  sun cilla makamai kan sojojin HKI a garin Rafa da ke kudancin ga kan iyaka da kasar Masar.

Labarin ya kara da cewa dakarun saraya Kudsu sun yi amfani da boma boman “bark’ a kan sojojin HKI wadanda suke Rafa na kudancin gaza, inda suka halaka wasu suka kuma raunata da dama daga cikinsu.

Dakarun saraya Kuds sun watsa wani faifen bidiyo wanda yake nuna irin ayyukan da suka yi na cilla makamai kan sojojin yahudawan.

A dayan bangaren kuma sojojin yahudawan sun ci gaba da cilla makamai masu linzami kan falasdinawa a wurare daban daban a gaza. Sannan a yau kai sun kashe falasdinawa akalla 10 a wurare daban daban a yankin.

Har’ila yau a wani labarin wanda tashar talabjin ta yahudawan ta watsa, ta nakalto wani mai sharhi kan labaran yaki mai suna Yuni bin Minakhim yana fadar cewa sojojin HKI ba sa kusa da samun kan mayakan Hamas, don har yanzun akwai dubban mayakan kungiyar wadanda suke karkashin kasa, kuma suna da makamai isassu wadanda zasu kai watanni suna fatawa da sojojin HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments