Kasar Cuba ta sanar da shiga cikin karar da kasar Afirka ta Kudu ta shigar kan Isra’ila a kotun kasa da kasa ta ACJ, da ke zargin gwamnatin Sahayiniya da aikata kisan kiyashi kan Falasdinawa a Gaza.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Cuba ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, kasar Cuba za ta bayar da goyon baya a hukumance kan korafin kisan kiyashin da kasar Afirka ta Kudu ta kai kan Isra’ila a kotun ICJ saboda yadda gwamnatin kasar ke ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula a Gaza.
Ma’aikatar Cuban ta bayyana matakinta na baya-bayan nan da tallafawa kokarin kasa da kasa na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar Palasdinu.”
Ma’aikatar ta ce “Kisan kare dangi, wariyar launin fata, tilastawa gudun hijira, da kuma azabtar da jama’a ba za su iya samun gurbi a duniyar yau ba, kuma kasashen duniya ba za su iya jurewa hakan ba.”
Cuba ta bi sahun Nicaragua, Kolombiya, Libya, Maldives, Masar, Ireland, Belgium, Turkiyya, da Chile a matsayin kasashen da suka yi niyya ko kuma suka sanar a hukumance su shiga cikin shari’ar da ake yi wa Isra’ila.
A watan Disambar 2023 ne Afirka ta Kudu ta shigar da kara kan Isra’ila a kan yakin da ta ke yi a zirin Gaza, na neman kotun ta Tilastawa Isra’ila dakatar da kisan kiyashin da takeyi a Gaza.
Daga nan ne kotun ta ICJ ta fitar da wani hukunci na farko da ya umurci Isra’ila da ta guji ayyukan da ka iya keta yarjejeniyar kisan kare dangi.