CNN: Mutane 8 Ne Su Ka Yi Kokarin Kashe Kawukansu A Kan Jirgin Yakin Amurka Na “Abraham Lincoln”

A wani rahoton da tashar talabijin ta CNN ta fitar ta bayyana cewa a lokacin da jirgin dakon jiragen yaki na "Abrahm Lincol" yake a
tambarin cnn

A wani rahoton da tashar talabijin ta CNN ta fitar ta bayyana cewa a lokacin da jirgin dakon jiragen yaki na “Abrahm Lincol” yake a gabas ta tsakiya a yaki da Iran, mutane 8 dake cikinsa ne su ka yi kokarin daukar rayukansu.

Ministan sojan Ruwan Amurka Hung Cao ya rubuta wata wasiki da a ciki yake bayar da jawabi ga ‘yar majalisar dattijai Kirsten Elizabeth wacce ta bukaci bayani akan halin da sojojin  ruwa suke ciki a jirgin ruwa na “Ibrahim Lincoln”.

Cao ya ce yunkurin kashe kan ya shafi matuka jirgi da ma’aikatan dake cikin jirgin Ruwan na Amurka.

Da akwai ma’aikata da yawansu yake tsakanin 6000 zuwa 7000 a karkashin rukuncin jiragen Ruwan na yaki su 6 da a jumlace su ne “Abraham Lincol”. Dadewar ma’aikatan akan doron ruwa na tsawon lokaci da ya wuce watanni 6 yana cikin abinda ya gajiyar da su.

Bugu da kari Iran ta rusa muhimmiyar cibiyar sojojin Ruwan Amurka dake Bahrai da can ne suke samun kayan abinci da  na gyara-gyaren jirgin da sauran kayan aiki.

Ma’aikatan dai sun yi kokarin kashe kawukansu ne ta hanyar jefa kansu a cikin teku, sai dai duk an tseratar da su.

 A shekarun baya ma dai an rika samun masu kashe kawukansu a cikin sojojin na Amurka kamar yadda rahotannin ma’aikatar yakin Amurka  “Pentagon” yake bayyanawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted