An cika rana ta 220 da fara kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza, inda ake ci gaba da samun shahidai musamman mata da kananan yara
Rahotonni sun bayyana cewa: Jiragen saman yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare kan yankuna daban-daban na Zirin Gaza a rana ta 220 da fara kai hare-hare kan yankin, lamarin da ke ci gaba da yin sanadiyar shahada Falasdinawa da dama tare da jikkatan wasu.
Rahotonnin sun jaddada cewa: Sansanin Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza a halin yanzu ya zama wuri mafi tsananin fuskantar luguden wuta a yankin, yayin da sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suke kara kai hare-hare da makaman masu linzami da kuma kai hare-hare ta sama kan sansanin, haka nan yankin Ma’akasar da ke arewacin yankin na Gaza.