China Ta Mayar Wa Da Amurka Martani Akan Girke Makamai Masu Linzami  A Kasar Philippine

Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar ta China Mao Ning ta bayyana cewa; Abinda wannan yankin na Asiya yake bukata shi ne sulhu

Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar ta China Mao Ning ta bayyana cewa; Abinda wannan yankin na Asiya yake bukata shi ne sulhu da zaman lafiya, ba makamai masu linzami na kai hari ba da haddasa tashe-tashen hankali.”

Haka nan kuma mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar ta China ta zargi Phillipine da hada kai da kasashen wajen saboda hargitsa zaman lafiya a yankin, kuma zai jawo gasa wajen kera makamai.

Makaman da Amurka ta girke a Phillipine su ne Typhon da suke cin matsakaicin zango, kuma na kai farmaki ne.

Har ila yau, mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar ta China ta kira yi Manila da ta saurari bukatun mutanen yankin da shi ne sulhu da zaman lafiya. Haka nan kuma ta bayyana matakin na kasar Phillipine da cewa kuskure ne mai kunshe da sakwanni marasa dadi ga sulhu da zaman lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments