China ta ce Ya Kamata A Aiwatar Da Sakamakon Taron Kolin Tianjin Don Inganta Kungiyar SCO

Kafofin yada labarai na duniya sun mayar da hankali kan taron majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar Shanghai SCO na 24 da aka gudanar kwanan nan

Kafofin yada labarai na duniya sun mayar da hankali kan taron majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar Shanghai SCO na 24 da aka gudanar kwanan nan a birnin Moscow na kasar Rasha.

 Fira ministan kasar Sin Li Qiang ya yi kira ga kungiyar SCO da ta aiwatar da shawarar inganta tsarin shugabanci na duniya da  kasar Sin ta gabatar, da karfafa kungiyar SCO a bangaren hadin kai da harkoki da kuma tasirinta.

Shekaru 24 da suka wuce bayan kafuwar kungiyar SCO, a karkashin jagorancin ruhin Shanghai, an samu habakar abotan kungiyar, da kara ingancinta, shi ya sa ma ta zama kungiyar yanki mafi girma a duniya, wadda ta kare muradun kasashe mambobin kungiyar, ta kuma inganta zaman lafiya da ci gaban duniya. A daidai sanda take ci gaba da samun bunkasa, kungiyar SCO tana kara taka rawar gani a harkokin duniya, inda ta fito da wata sabuwar hanya dake hada kowa a cikinta, wanda hakan ya ba da misali ga samun ingantaccen tsarin shugabancin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments