Search
Close this search box.

China Ta Bukaci Kawo Karshen Adawa Da Bukatar Zamar  Falasdinu Mamba Na Din Din Din A Majalisar Dinkin Duniya

Kasar China ta bukaci a daina adawa da shigar Falasdinu cikin Majalisar Dinkin Duniya a matsayar mamba na din din din Kakakin ma’aikatar harkokin wajen

Kasar China ta bukaci a daina adawa da shigar Falasdinu cikin Majalisar Dinkin Duniya a matsayar mamba na din din din

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar China Wang Wenbin a yau litinin ya bayyana cewa: Akwai bukatar kawo karshen adawa da neman baiwa Falasdinu damar zama mamba na din din din a Majalisar Dinkin Duniya, yana mai kira ga kasashen da abin ya shafa da kada su ci gaba da adawa da halin kirki da jin kai na kasashen duniya. Wannan kira na kasar China ya zo ne gabanin kada kuri’a kan wannan batu a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya.

Kasar China ta kara da cewa: Kada wasu kasashe su ci gaba da kawo cikas ga shawarwarin da suka shafi shigar Falasdinu Majalisar Dinkin Duniya a matsayar mamba na din din din.

A yayin zaman babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, kasashe 143 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudurin neman zamar Falasdinu mamba na din din din a Majalisar Dinkin Duniya, yayin da kasashe 9 suka nuna adawa da shi, ciki har da Amurka, sannan wasu kasashe 25 sun kaurace wa kada kuri’a, ciki har da Birtaniya, a cewar shafin yanar gizon Majalisar Dinkin Duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments