Canada Ta Ayyana Kungiyar ‘Yan Houthi Ta Yemen A Matsayin Ta Ta’addanci

Gwamnatin Canada ta sanya kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan Houthi a kasar Yemen a matsayin ta ‘yan ta’adda, wani mataki da

Gwamnatin Canada ta sanya kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan Houthi a kasar Yemen a matsayin ta ‘yan ta’adda, wani mataki da tuni masana suka fara bayyana shi a wani sabon yunkuri na nuna adawa da kungiyoyin ‘yan gwagwarmaya dake yaki da ta’addanci a fadin yankin yammacin Asiya.

Canada dai na mai adaawa da matakan da ‘yan Houtsi na Yemen ke dauka na goyan bayan al’ummar falasdinu dake fuskantar zalincin Isra’ila.

Ministan Tsaron Jama’a na Canada Dominic LeBlanc ya sanar a ranar Litinin cewa matakin “yana ba da gudummawa ga kokarinmu na yaki da ta’addanci a duniya da kuma daidaita Canada da kawayenmu.”

Ya zargi Ansarullah da aikata “ayyukan tsattsauran ra’ayi da ta’addanci,” yana mai cewa, “Za mu ci gaba da daukar matakan dakile yaduwar wadannan ayyukan a duniya da kuma dakile barazana ga Canada, ‘yan kasarta, da muradunta a duniya.”

Sanarwar ta kara da cewa, “Ansarallah na da alaka ta kut-da-kut da Dakarun Kare Juyin Juyin Juya Halin Musulunci na Qods Force da Hizbullah.

Sannan ta yi nuni da ayyukan kyamar Isra’ila da kungiyar ke yi, wanda ke nuna hare-haren da take kaiwa jiragen ruwa na Isra’ila da kuma jiragen da ke kai kayayyaki da suka hada da na soji ga gwamnatin Isra’ila.

Ansarullah dai na neman hanyoyin dakile tattalin arzikin Tel Aviv don dakatar da yakin da take yi na kisan kare dangi a zirin Gaza tun a watan Oktoban 2023 wanda ya zuwa yanzu ya lakume rayukan Falasdinawa akalla 44,466, galibi mata da kananan yara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments