Burkina faso ta musanta labaren da ake yayatawa na aikata kisan kiyashi a arewacin kasar.
Ministan Tsaron kasra na mayar da martani ne ga labarin da aka buga a wannan Alhamis, na RFI, na kisan kiyashi da kungiyar sa kai ta kasar (VDP) ta yi a kauyukan Dori da Gorgadji.
Ministan Tsaron Burkina Faso ya ce “mummunan zarge-zarge ne kawai ake wa kasar da nufin “dagula zaman lafiyar kasar” da kuma “bata sunan” sojojin da VDP.
Ya ci gaba da yin kira ga al’ummar Burkina Faso da su yi taka-tsan-tsan game da bayanan “farfaganda” da ke da nufin haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummomin kasar.
A cikin sanarwar da ya fitar, Céletin Simporé, ya sake nanata kudurin gwamnati na “kare fararen hula da mutunta hakkin dan Adam.