Brazil: Masu Rajin Kare Hakkin Bil’adama Sun Bukaci A Kawo Karshen Yakin Gaza

Kungiyoyi daban-daban a kasar Brazil kama da yan siyasa, masu rajin kare hakkin bil’adama, masu kuma goyon bayan Falasdinawa sun taru a ofisoshin jakadancin Amurka

Kungiyoyi daban-daban a kasar Brazil kama da yan siyasa, masu rajin kare hakkin bil’adama, masu kuma goyon bayan Falasdinawa sun taru a ofisoshin jakadancin Amurka da kuma kananan ofisoshin nata a Rio De Janeiro, Recife, da Brasília  a duk fadin kasar suna bukatar a kawo karshen yakin da ke faruwa a Gaza, da kuma katse dangantaka da HKI.

A dai dai lokacinda yuwan take kara tsanani a cikin falasdinawa a Gaza, mutanen kasar Brazil sun bukaci gwamnatin kasar ta dauki matakai na katse dangantaka da HKI da kuma Amurka wacce take goyon bayanta a kan kissan kiyashin da take aikatawa a gaza.

Tun lokacinda daliban Jami’o’ii a kasar Amurka suka fara zanga0zangar goyon bayan falasndinawa a gaza a cikin watan Octoban shekara ta 2023, zanga zangar ta watsu a mafia yawan kasashen duniya. Sun allawadai da HKI da kuma kasashen yamma masu goya mata baya, musamman Amurka.

Masu zanga zanga a Brazil sun bukaci gwamnatin kasar ta dakatar da duk wata hulda da HKI wadanda suka hada da kasuwanci diblomasiyya, sannan yi watsi da shirin Amurka na kudaden fito.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted