Ministan harkokin wajen iran Abbas Araqchi da takwararsa ta kasar birtaniya sun tattauna ta wayar Tarho inda suka tattauna kan batutuwa da suka shafi dangantaka tsake tsakanin da suka shafi huldar diplomasiya.
Kasahen birtaniya da jamus da faransa sun dauki mummunan mataki kan shirin nukiliyar Iran, sun matsa lamba kan sanya takunkumi fiye da bukatar dokokin kasa da kasa, wanda haka ya kara ruruta wutar rashin yarda a terhran, da kuma kara rikita kokarin da ake yi na ganin an cimma wata matsaya.
Shirin nukiliyar iran na zaman lafiya ne kuma yana karkashin dokar hana yaduwar makaman nukilya wanda ya amince da hakkin iran na bunkasa shirinta na nukiliya domin samar da makamashi
Ministan harkokin wajen iran yayi suka game da matakin rashin girmamawa da kasashen turai 3 suka dauka wato jamus, faransa da kuma birtaniya kan shirin nukiliyar iran, yace iran tana maraba da duk wata tattaunawa bisa mutunta juna da kare hakki da doka ta bayar, da kuma maslahar kasa, amma ba za ta amince da tattaunawa ta bangare daya ba kawai.