Bin Farhan: Babu Batun Kulla Alaka Tsakanin Saudiyya Da Isra’ila Sai An Kafa Kasar Falastinu

Ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan ya fada a jiya Alhamis cewa, babu batun daidaita alaka tsakanin Saudiyya da Isra’ila a halin yanzu, har

Ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan ya fada a jiya Alhamis cewa, babu batun daidaita alaka tsakanin Saudiyya da Isra’ila a halin yanzu, har sai an cimma matsaya ta kafa kasar Falastinu mai cin gashin kanta.

A yayin zaman tattaunawa a shirin zuba jari a birnin Riyadh na Saudiyya, ministan harkokin wajen kasar ya ce, “Ba batun daidaita al’amura ba ne kawai ke cikin hadari a halin yanzu,  halin da ake ciki a daukacin yankin babu bushara da alheri matukar dai ba a sami mafita da ta dace ba,  ya kara da cewa, “Muna aiki tukuru don tabbatar da cewa Palasdinawa sun sami hakkikinsu, kuma Palasdinu ta zama mamba a cikin kasashen duniya a hukumance.”

Ya kara da cewa, “Ina fatan mahukunta a Isra’ila za su gane cewa wannan ba abu ne mai kyau kawai ta fuskar adalaci ba,  har ma ga tsaro da kuma manufofin Isra’ila a yankin gabas ta tsakiya.

Dangane da alakar Saudiyya da Iran kuwa, Bin Farhan ya tabbatar da cewa dangantakar kasashen biyu tana tafiya daidai.

Ministan harkokin wajen Saudiyya ya kuma bayyana cewa kafa kasar Falasdinu yana da alaka da ka’idojin dokokin kasa da kasa, ba wai amincewar Isra’ila kawai ba, kuma kasa aiwatar da hakan na nuni da gazawa daga bangarri na kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments