Bankin Duniya ya amince da bayar da rancen kudade fiye da dala biliyan daya da rabi ga gwamnatin Najeriya.
A wata sanarwa da ya fitar a wannan Litinin Bankin Duniya ya bayyana cewa, ya amince da bayar da rance ga Najeriya domin karfafa gwiwar gwamnatin tarayyar kasar wajen gina ma’aikata da inganta harkokin kiwon lafiya ga mata da yara da kuma tsofaffi.
Bankin ya ce rancen ya hada da dala miliyan 500 don magance matsalolin shugabanci da ke kawo cikas ga ilimi da kiwon lafiya, dala miliyan 570 na kiwon lafiya a matakin farko, da kuma wasu dala miliyan 500 don samar da makamashi mai tsafta da yakar illolin da fari ke haifarwa a kasar.
Sanarwar ta kara da cewa ayyukan da aka amince da su za su taimaka wajen magance illolin sauyin yanayi kamar ambaliyar ruwa da fari ta hanyar karfafa madatsun ruwa da kuma fari.
“Bankin Duniya a yau ya amince da bada lamuni guda uku da suka kai dala biliyan 1.57 domin taimakawa gwamnatin Najeriya.