Babban jami’in diplomasiyyar Iran Ali Bakiri Kani ya sanar da cewa; HKi ta ketare iyaka, saboda kisan gillar da ta yi wa Isma’ila Haniyya shugaban kungiyar Hamas a cikin kasar Iran, don haka mayar da martani mai tsanani yana nan tafe.
Babban jami’in diplomasiyyar na Iran ya bayyana hakan ne a yayin da ya tattauna ta wayar tarho da mataimakin fir minister kuma ministan harkokin wajen Pakistan Muhammad Ishak Dar.
A yayin wannan tattaunawar shugaban diplomasiyyar na Iran ya jinjinawa kasar Pakisran saboda irin matakan da take dauka dangane da batun Falasdinu.
A gefe daya,babban jami’in diplomasiyyar na kasar Paksistan ya jinjinawa Iran saboda kiran da ta yi akan a yi taron gaggawa na kungiyar kasashen musulmi domin tattauna kisan da HKI ta yi wa Shahid Isma’ila Haniyyah.
Ali Bakiri ya kuma ce; Abinda zai faru shi ne mayar da martani daga Iran wanda babu taraddudi a cikinsa, sannan kuma bai kamata a ce kasashen musulmi sun yi shiru ba tare da sun motsa ba akan yadda ‘yan sahayoniyar suke haddasa riciki da yamutsi a cikin wannan yankin.