Babu Wani Zabi Da Ya Rage Face Amincewa Da Iran A Matsayin Cibiyar Kimiyyar Masana’antar Nukiliya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa yanzu babu abin da ya ragewa kasashen yamma banda su amince da Iran a matsayin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa yanzu babu abin da ya ragewa kasashen yamma banda su amince da Iran a matsayin cibiyar kimiyyar masa’antu ta shirin nukiliya na zaman lafiya.

Ministan ta fadi hakan ne a wata ziyara da ya kai hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar,  inda ya bayyana irin namijin kokarin da suke yi wajen kara inganta nukiliyar masana’antu, kuma yace kasarsa ba za ta taba yin watsi da shirin ta na nukiliya domin ayyukan zaman lafiya ba.

Haka zalika ya jinjinawa iran game da irin gagarumin ci gaban da suka samu a fasahar nukiliya, inda suka shiga bangare masana’antu da ya yadu zuwa wasu bangarori daban daban.

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta gudanar da bincike sau tarin yawa tun bayan harin da Amurka da isra’ila suka kai, a makon jiya hukumar ta sanar cewa baa bata damar kutsawa zuwa tashoshin nukiliyar Fardow da Natanza da Isfahan ba inda Amurka ta yi wa ruwan wuta a ranar 22 ga watan yuli wanda hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar NPT

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments