Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kudiri da ya yi kira da a kawo karshen yakin kisan kare dangi da gwamnatin Isra’ila ke yi tun daga watan Oktoban shekarar 2023 a zirin Gaza.
Kasashe 158 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudurin a wannan Laraba, yayin da kasashe 9 suka ki amincewa da kudirin, daga cikinsu kuwa hard a Amurka, yayin da wasu kasashe 13 suka kauracewa kada kuri’a.
Kudurin ya bukaci “a tsagaita bude wuta a Gaza cikin gaggawa ba tare da wani sharadi ba kuma na dindindin, inda sanadiyyar wannan yaki na Haramtacciyar Kasar Isra’ila a kan al’ummar Gaza, ya zuwa yanzu akalla Falastinawa 44,805 ake da tabbacin sun rasa rayukansu, galibinsu mata da kananan yara.
Robert Wood, mataimakin wakilin Majalisar Dinkin Duniya ya ce zai zama “abin kunya da kuskure” yin amfani da hakkin hawa kujerar naki a kan wannan kudiri.
Washington, wadda ta yi amfani da ikonta na hawa kujearr naki a duk lokacin da aka bukaci Isra’ila ta kawo karshen kisan kiyashi Gaza, tare da yin fatali da irin wadannan kudurori a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ta yi ikirarin cewa yuwuwar dakatar da yakin zai iya sa kugiyoyin gwagwarmayar Falasdinu su ki sakin fursunonin da suke tsare da su.