Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya yayi kashedin kan wani lamari mai matukar hadari da ya tabaibaye Labanon!
Ajawabinsa na bude zaman taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya tare da muhawarar shekara-shekara, Gutarres ya ce: A yau mun fuskanci cin zarafi da hare-haren wuce gona da irin haramtacciyar kasar Isra’ila kan Gaza da Lebanon, kuma zaman lafiya shi ne taken dukkanin jawaban da aka gabatar, wanda na farko shi ne jawabin shugaban babban zauren Majalisar Dinkin Duniya.
Philemon Yang, ya yi kira da a dauki mataki na hadin gwiwa don samar da zaman lafiya da wadata, ba wai a mayar da albarkatun kasa zuwa taskar yaki da sojoji da ke amfani da ita wajen rura wutar kere-keren makamai da ba a taba ganin irinsu ba tun lokacin yakin cacar baki.
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce barkewar yakin basasa a yankin yammacin Asiya ba shi da wata maslaha ga kowa, yana mai jaddada cewa diflomasiyya ita ce hanya daya tilo ta tabbatar da tsaro, yana mai kawar da kai kan irin rawar da kasarsa ke takawa wajen tallafawa haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar dabarun soja da kuma muggan makamai.