Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ya Bayyana Takaicinsa Kan Abin Da Ke Faruwa A Gaza

Zaman taron tunawa da harin guguwar Al-Aqsa, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya ce; Yakin Gaza yana rusa rayuwar Falasdinawa Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Zaman taron tunawa da harin guguwar Al-Aqsa, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya ce; Yakin Gaza yana rusa rayuwar Falasdinawa

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana cewa: Yakin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi a Zirin Gaza da aka fara shekara guda da ta gabata, yana ci gaba da rusa rayuwar Falasdinawa tare da wurga su cikin mummunar wahala.

Babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada a cikin wani sakon bidiyo da ya aike a yayin bikin cikar shekara guda da fara yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan Zirin Gaza, ya bukaci kasashen duniya da su mai da hankali kan munanan al’amuran da suka faru tun bayan ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023.

Guterres ya bayyana goyon bayansa da alhininsa ga wadanda yakin ya shafa da kuma ‘yan uwansu.

Ya kara da cewa: Lokaci ya yi da za a sako fursunoni tsakanin bangarorin biyu, da ajiye makamai gefe guda, da kuma dakatar da wahalhalun da yankin ke fuskanta, kuma yanzu lokaci ne na gudanar da zaman lafiya da aiwatar da dokokin kasa da kasa da kuma wanzar da adalci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments