Babban Kwamandan sojojin Iran ya jaddada cewa: Rundunar sojin Iran ta tabbatar da cikakken shirinta na tunkarar duk wani yaki mai sarkakiya
Babban Kwamandan Sojojin Iran, Manjo Janar Amir Hatami, ya yi alƙawarin cewa: Sojojin Iran za su kare ‘yancin kasar, mutuncin yankunanta, da kuma Jamhuriyar Musulunci “har zuwa ƙarshen numfashinsu,” yana mai jaddada cikakken shirinsu na fuskantar duk wani yaƙi mai fuskoki da dama wanda ya shafi fannoni daban-daban na siyasa, tattalin arziki, da kuma tunani.
Manjo Janar Hatami ya tabbatar cewa: Alhakin rundunar soji a cikin yanayin da ake ciki, idan aka yi la’akari da canje-canje da ci gaba da ake samu, babu shakka yana da matuƙar muhimmanci kuma yana da matuƙar nauyi.
Ya yi nuni ga ikirarin makiya na samun nasara ga manufarsu, yana mai cewa wadannan ikirarin karya ne kuma ba su da tushe. Wadannan makiya sun yi yakin shekaru 20 a Vietnam da Afghanistan kafin su janye da shan kaye, kuma sun fuskanci irin wannan mummunan sakamako a Iraki da sauran kasashe. Suna shiga fagen fama da barazana da tsoratarwa, amma suna ficewa cikin jin kunya. Saboda haka, rashin nasarar makiya ba makawa, amma cimma wannan burin yana bukatar fahimtar yanayin da duniya ke ciki a yanzu da kuma juriya da jajurcewa daga bangaren al’ummar Iran.