Babban Jami’in Kungiyar Hamas Ya Karyata Batun Mika Fursunonin Isra’ila Cikin Sa’o’i 72

Babban jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Mika fursunoni da gawarwaki cikin sa’o’i 72 ba gaskiya ba ne a halin da ake ciki yanzu. Babban

Babban jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Mika fursunoni da gawarwaki cikin sa’o’i 72 ba gaskiya ba ne a halin da ake ciki yanzu.

Babban jami’in kungiyar Hamas Musa Abu Marzouk ya tabbatar a ranar Juma’a cewa, batun mika fursunoni da gawarwakin yahudawan sahayoniyya cikin sa’o’i 72 lamari ne na nazari, ba tabbas ba, a halin da ake ciki yanzu.”

Abu Marzouk ya bayyana cewa: Kungiyar Hamas ta amince da shirin Amurka da aka gabatar “a bisa ka’ida,” yana mai cewa “aiwatar da shi yana bukatar tattaunawa.” Ya kuma lura da cewa dukkan bayanai da suka shafi rundunar wanzar da zaman lafiya “yana bukatar fahimtar juna da fayyace shi dalla-dalla.”

Dangane da batun makamai kuwa, Abu Marzouk ya bayyana a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Aljazeera cewa: Kungiyar Hamas za ta mika makamai ga gwamnatin Falasdinu da za a kafa nan gaba, yana mai jaddada cewa duk wanda ke mulkin Gaza zai mallaki makamai. Ya kara da cewa kungiyar za ta shiga tattaunawa kan dukkan batutuwan da suka shafi batun kungiyar da kuma makamai.

Babban jami’in na Hamas ya bayyana cewa: Kungiyar “ta amince da wani ra’ayi na yanki da kasa da kasa da Masar ta gabatar,” tare da lura da cewa wannan hangen nesa “ya hada da amsoshi game da zaman lafiya da kuma al’amuran nan gaba.”

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta sanar a yammacin jiya Juma’a cewa ta mika martaninta ga shirin shugaban Amurka Donald Trump na dakatar da yakin zirin Gaza ga masu shiga tsakani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments