Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a fagen goyon bayan hakkokin Falasdinawa da gwagwarmayarsu, yana mai jaddada cewa: Shahidin al’ummar Sayyed Hassan Nasrallah ya gabatar wa Falasdinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya ambata ba.
A cikin wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Alam, Adaya ya yi cikakken bayani kan yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da yahudawan sahyoniya, yana mai jaddada cewa: Gwagwarmaya tana ci gaba da tafiya a kan tabbataccen matsayi domin cimma manufofinta duk kuwa da kalubalen da ake fuskanta.
Har ila yau ya tabo matsayar da ‘yan gwagwarmaya suke fuskanta na makircin kasa da kasa da ke yunkurin raba al’ummar Falastinu da tushensu na asali, yana mai jaddada cewa: Tsayin dakan ‘yan gwagwarmaya da hadin kansu sune mafi girman makamai wajen tunkarar duk wani makircin wuce gona da iri kan al’ummar Falasdinu.