Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya sanar da shirin kai ziyara birnin Tehran nan da makwanni masu zuwa a yayin da ake ci gaba da tattaunawa don tsaida takamaimen lokacin.
Ziyarar ta zo ne a wani bangare na ci gaba da huldar diflomasiyya tsakanin Iran da hukumar IAEA, da nufin tinkarar batutuwan da suka shafi Nukiliya, da samar da hadin gwiwar fasaha cikin tsarin alkawurran da Iran ta dauka a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT).
Ziyarar ta kuma jaddada irin hadin gwiwar da Tehran ke ci gaba da yi da hukumar ta IAEA, duk da matsin lamba daga waje da kuma zargin siyasa daga kasashen yammacin Turai.
Da yake amsa tambaya daga wakilin TASS, Grossi ya tabbatar da cewa ana tattaunawa don tsara ziyararsa a makonni masu zuwa.
Wannan bai ta ce ziyarar Rafael Grossi, t afarko a Iran ba, don kuwa ko a kasrhen watan Nuwamban bara ya gana da shugaban Iran Masoud Pezeshkian da ziyarce-ziyarcen cibiyoyin nukiliya na Fordow da Natanz.
Ziyarar Grossi ta zo ne a daidai lokacin da Iran ke ci gaba da tabbatar da hakkinta na samar da makamashin nukiliya cikin lumana karkashin dokokin kasa da kasa.