Rahotanni sun bayyana cewa lindsy Graham fitacce dan majalisa a congress din Amurka kuma na hannun daman shugaban kasar Amurka Donald Trump kuma babban abokin burmin HKI ya mutu kwatsam a yammacin jiya Asabar yana da shekaru 71 a duniya
An zabi Graham ne a matsayin dan majalisa a Amurka a shekara ta 2002 kuma ana sake zaben sa a shekara ta 2008da 2014 da 2020, a shekara ta 1994 an zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai daga gundumar majalisa ta 3 ta kudancin Carolina .
A baya bayan nan yayi aiki a matsayin shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattijai, da dai sauran mukamai da ya rike, ya kasance mai goyon bayan yaki da aka kaddamar kan kasar Iraqi kuma yana daga cikin wadanda suka kara tunzurawa wajen ganin an dauki matakin soji kan kasar Iran.
Ministan tsaron HKI ya fadi a yau lahadi cewa suna cikin jimamin mutuwar Graham wanda ya kasance tare da isra’ila a lokaci mafi tsanani.