Ma’aikatan lafiya a Gaza sun kwashe Falasɗinawa majinyata daga Asibitin al-Ahli Baptist bayan rundunar sojin Isra’ila ta yi gargaɗi ga mutane su fice daga yankunan Al-Daraj, Al-Tuffah da Tsohon Birni da ke Birnin Gaza.
Wata majiya a asibitin da ta yi magana da kamfanin dillancin labarai na Anadolu Agency ta ce tawagar ma’aikatan kiwon lafiya ta kwashe majinyata da sauran masu ƙananan larurori daga asibitin zuwa wata cibiyar kula da lafiya da ke arewacin Gaza.
Majiyar ta ce Isra’ila ta tura jirage marasa matuƙa da yawa yankin da asibitin yake, inda suka riƙa buɗe wuta kan fararen-hula abin da ya sa ma’aikatan asibitin kwashe majinyatar.
Tun da farko, jiragen yaƙin Isra’ila da sun yi ta kai hari a wasu yankunan Birnin Gaza, inda suka jikkata gomman mutane tare da korar dubban iyalai daga gidajensu, a daidai lokacin da sojojin na Isra’ila suka umarci mutane su fita daga gidajensu.