Search
Close this search box.

Ayatullahi Khatami Ya Jaddada Matsayin Farin Jinin Shugabannin Iran A Wajen Al’ummarsu

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran ya ce: Taron jama’a wajen jana’izar shahidai masu hidima ga al’umma yana nuna irin farin jinin

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran ya ce: Taron jama’a wajen jana’izar shahidai masu hidima ga al’umma yana nuna irin farin jinin gwamnatin Jamhuriyar Musulunci

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, Ayatollah Ahmad Khatami, ya jaddada cewa: Hallarar jama’a wajen jana’izar shugabanni shahidai masu hidima ga al’umma a garuruwa daban-daban na kasar Iran yana nuna farin jinin gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ne karara.

A cikin hudubar Juma’arsa ta yau Ayatullah Ahmad Khatami ya kara da cewa: Al’ummar Iran sun bayyana mubaya’arsu ga gwamnatin Musulunci ta hanyar gagarumin halartar jana’izar shugaban kasa Sayyid Ibrahim Ra’isi da mukarrabansa da kuma nuna hadin kai da fahimtar juna a tsakaninsu.

Ayatullah Khatami ya ci gaba da cewa: Idan aka gudanar da zaman makoki a dukkanin garuruwan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, to dukkanin al’ummar Iran za su fito kwansu da kwar-kwatarsu domin jaddada mubaya’arsu ga shugabanninsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments