Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yaba wa marigayi shugaban kungiyar Hamas Yahya Sinwar bisa gagarumin aikinsa wajen tunkarar ‘yan mamaya masu zagon kasa, yana mai bayyana shi a matsayin wani mutum mai tasiri a gwagwarmayar falastinawa.
A cikin sakon da ya aike a ranar Asabar, kwana guda bayan da kungiyar Hamas ta tabbatar da shahadar Sinwar, Ayatullah Khamenei ya mika ta’aziyyarsa ga iyalansa, da ‘yan uwansa, da dukkan wadanda suka sadaukar da kansu wajen jihadi don neman yardar Allah.
“Ya kasance mutum mai juriya da gwagwarmaya ya tsaya tsayin daka wajen yakar abokan gaba masu zalunci.” Kamar yadda jagoran ya rubuta.
“Da hikima da jajircewa, ya rusa makiya da karfi, inda ya bar tarihi na guguwar aqsa, sannan cikin daukaka da alfahari ya samu shahada wajen kare gaskiya da yaki da makiya Allah.
Jagoran ya kuma jaddada halin da ake ciki da cewa, duk da rashin jagororin gwagwamaya manya da aka yi, amma kuma hakan ba zai iya kawar da gwagwarmaya da zaluncin ma’abota girman kai ba.