Ayatollah Khamenei: Mahangar kare hakkin dan Adam ta  yamma tana da matsala 

2024 Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatollah Sayyid Ali  Khamenei ya gana da shugaban ma’aikatun shari’a da manyan jami’anta. A farkon wannan taro jagoran ya

2024 Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatollah Sayyid Ali  Khamenei ya gana da shugaban ma’aikatun shari’a da manyan jami’anta.

A farkon wannan taro jagoran ya karrama shahidan bangaren shari’a da suka hada da shahidi Beheshti, da kuma shahidi Raisi wanda ya yi fice a fannin shari’a, ya kuma mika godiya ta musamman kan kokarin shugaban sashen shari’a na yanzu, da jami’ai, alkalai, da ma’aikata a cikin wannan na’urar.

Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa Alkur’ani mai girma da sauran nassosin Musulunci suna mayar da hankali matuka kan batun lamarin “Adalci”, Jagoran ya dauki jaruntaka a matsayin wajibcin aiwatar da adalci, ya kuma ce: Kamar yadda ya jaddada cewa, Dole ne hukumar shari’a ta yi aiki ta yadda makiyinta zai ya yanke kauna daga daga gani duk wani zalunci a cikin ayyukanta.

Ya jaddada cewa alkalai sun dogara ne da dokokin cikin gida, ba majiyoyin kare hakkin bil’adama na yammacin duniya ba, da kuma ci gaba da ziyarar aiki da shugaban hukumar shari’a ke yi, da kuma bibiyar aiwatar da shawarwarin da aka sanya a gaba a yayin wadannan ziyarce-ziyarcen. Sauran batutuwan da jagoran ya jaddada sun hada cewa, “Ku yi aiki ta hanyar da ta dace, domin kuwa ra’ayin jama’a yana kallon shari’a a matsayin gidan adalci kuma cibiyar tabbatar da hakkoki ba tare da sassauci ba.”

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da shawartar alkalai da su guji dogaro da tushe na hakkin dan Adam na yammacin duniya a cikin hukunce-hukuncen nasu, ya kuma ce: Tushen kare hakkin bil’adama na yammacin Turai ba daidai yake ba, kuma su da kansu ba sa aiwatar da su, kuma a yau kowa sheda ne kan hakan a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments