Asusun kula da kananan yara “UNICEF” ya bayyana cewa: Dole ne a kare makarantu da matsugunan ‘yan gudun hijira sannan a daina cin zarafin yara
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya jaddada cewa: Dole ne a kare makarantu da matsugunan ‘yan gudun hijira, kuma dole ne a daina cin zarafin yara.
Asusun “UNICEF” a shafinsa na dandalin ‘X” a jiya Asabar ya bayyana cewa: An samu munanan rahotanni masu daga hankula na wani harin da aka kai a safiyar jiya Asabar kan wata makaranta a Gaza da ke dauke da ‘yan gudun hijira, da kuma rahoton kashe yara da jikkatan wasu a wani wuri da suka fake suna da tabbacin suna cikin aminci.
A jiya Asabar ce; Sojojin gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai wani sabon harin kisan kiyashi kan makarantar Al-Ta’bi’een da ke dauke da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da suka rasa matsugunansu a unguwar Al-Daraj da ke birnin Gaza, lamarin da ya yi sanadin shahadan mutane sama da 100 tare da jikkatan wasu daruruwa na daban.