Araqchi Ya Gana Da Babban Malamin Yahudawa Mai Adawa Da ‘Yan Sahayoniyya A Gefen Taron Kungiyar BRICS

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da babban malamin yahudawa rabbi mai adawa da ‘yan sahayoniyya a gefen taron BRICS a Brazil Ministan harkokin

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da babban malamin yahudawa rabbi mai adawa da ‘yan sahayoniyya a gefen taron BRICS a Brazil

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gana kuma ya zanta da wani babban malamin yahudawa mai adawa da ‘yan sahayoniyya a gefen taron kasashen BRICS a kasar Brazil.

Rabbi Yisrael Dovid Weiss, wanda ya je Brazil domin ganawa a gefen taron BRICS, ya gana da ministan harkokin wajen Iran, inda suka yi musayar ra’ayi da shi.

Wani abin lura shi ne cewa a baya malamin ya ziyarci ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke kasar Brazil bayan bude littafin ta’aziyya ga shahidan da yahudawan sahayoniyya da suke kai wa hari a                                                                    kasar hari. A cikinsa ne ya rubuta kalamai na nuna goyon bayansa ga al’umma da gwamnatin Iran tare da jajantawa iyalan shahidan da suka rasa rayukansu sakamakon zaluncin da yahudawan sahayoniyya suka dauka kan kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted