rahotanni sun bayyana cewa minstan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi yayi watsi da zargin da Trump yayi na mutuwar mutane 32000 a lokacin tarzomar da aka yi a iran na tsawon kwanaki biyu,a fadin kasar , kuma ya bukataci ta gabatar da hujja dake tabbatar da zargin nasa,
ministan ya wallafa a shafinsa na X a yau Asabar cewa saboda alkwarin da muka yi na bayyana gaskiyar abin da ya faru, tuni, gwamantin kasar iran ta buga bayani game da wadanda harin ta’adanci ya shafa kusan mutane 3117 ciki har da jami’an tsaro kusa guda 200.
kasar Amurka da Isra’ila suna da hannu a zanga zangar da ta faru a iran inda tsohon sakataren tsaron Amurka mike Pompeo ya wallafa a shafinsa na twita a lokacin cewa barka da sabuwar shekara ga dukkan iraniyawa da suka fito kan tituna, kuma yace dukkan ma’aikatan Mussad sunatare da su.