Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci yana kan hanyar zuwa birnin Geneva, domin bude tattaunawa karo na uku da Amurka a gobe Alhamis.
Da marecen yau Laraba ne dai ministan harkokin wajen na Iran ba bar binrin Tehran, tare da tawagar da take rufa masa baya, zuwa kasar Switzerland da can ne wurin da za a yi tattaunawar bayan fage da Amurka da ofishin jakadancin kasar Oman zai karbi bakuncinta.
Gabanin barinsa birnin Tehran, ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana cewa; Bisa tattaunawar da aka yi a baya, Iran za ta je wannan tattaunawar ta yanzu ne cikin Azama da niyyar ganin an cimma matsaya ta adalci a cikin kankanen lokaci mai yiyuwa.