Araghchi: Iran na da nata hanyoyin na kare tashoshinta na nukiliya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya gargadi gwamnatin sahyoniyawa game da yin duk wani gigi na yin shsihigi a kan tashoshin nukiliyarta,  yana

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya gargadi gwamnatin sahyoniyawa game da yin duk wani gigi na yin shsihigi a kan tashoshin nukiliyarta,  yana mai jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dogara ne da kayan aikin soja na cikin gida da kuma hanyoyin da za ta kare kanta daga duk wani yunkurin wuce gona iri na makiya.

Araghchi ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a birnin Kuwait babban birnin kasar Kuwait a wannan Talata.

“Isra’ila ba ta daina aikata kowane irin laifi ba har ya zuwa yanzu. Abin takaicin shi ne, tana ci gaba da aikata irin wannan ta’asa tare da goyon bayan Amurka da wasu kasashen Turai.

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya ce “Wasu daga cikin wannan ta’asa ana daukarta a matsayin laifin yaki kuma ana iya bin kadunsu a kotun kasa da kasa.”

Ya jaddada cewa Isra’ila ba ta aiki da ka’idojin kasa da kasa, yana mai cewa, dakatar da zalunci ta kowace hanya bai sabawa kaidoji da dokokin kasa da kasa ba.

“Idan aka kai hari ga muhimman ababen more rayuwa na cikin kasar Iran, abokan gaba na Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun san abin da za mu iya yi don mayar da martani,” in ji Araghchi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments